‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun shiga garin Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori inda suka kwashe mutane da dama a ciki harda tsohon shugaban hukumar masu yiwa ƙasa hidima Birgediya Janar Maharazu Tsiga.
Wani mazaunin garin da baya so a faɗi sunan sa yace ‘yan bindigan sun kashe ɗan uwan nasu bisa karya dokar su na kada ayi harbi amma yayi ta harbi a gidan Birgediya Tsiga.
Wani mazaunin garin da baya so a faɗi sunan yace basu kashe kowa ba sai da wani ɗan uwan su yan bindigan bayan sun same sa da karya dokar hana yin harbi a cikin gari.
Yace ɗan bindigan da aka kashe yayi ta harbi a gidan Birgediya Tsiga wanda hakan bai masu daɗi ba,”nan take suka harbe shi,suka tafi da gawar.
Ya zuwa yanzu babu wani bayani daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin Jihar Katsina.
