El-Rufai ya magantu kan rikicin Ribadu da Naja’atu

Spread the love

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya mara wa Najaatu Mohammed baya a rikicinta da mai ba shugaban ƙasa shawara Kan tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. El-Rufai ya bayyana cewa takardun majalisar dattawa da na zaman majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) na shekarar 2006 za su tabbatar da maganganun da ake zargi Ribadu ya yi a wancan lokaci.

A cewar El-Rufai, rahoton jaridar Daily Trust na watan Fabrairun 2007 ma yana tabbatar da wannan batu. Ya buƙaci masu ikon samun takardun gwamnati su nemi takardun zaman majalisar Zlzartaswa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) domin tabbatar da gaskiya.

El-Rufai ya ƙara da cewa a zaman FEC na musamman da aka yi a shekarar 2006, inda shi ma ya halarta, hukumar EFCC ƙarƙashin jagorancin Ribadu ta gabatar da irin waɗannan zarge-zarge kan wasu manyan jami’an gwamnati. Ya ce lokaci ya yi da mutane za su faɗi gaskiya, domin a wasu lokuta shiru ba shi da amfani ga kasa.

By ukarofi