‘Yan sanda sun tabbatar da tserewar mutum biyu da ake zargi da garkuwa da wani ɗan majalisa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra a ranar Talata ta tabbatar da tserewar wasu mutum biyu da aka kama dangane da sacewa da kisan ɗan majalisar dokoki na Jihar Anambra mai wakiltar Onitsha North 1, marigayi Hon. Justice Azuka. Azuka ya ɓace ne a ranar 24 ga Disamba, 2024, a lokacin da yake komawa Onitsha don bukukuwan Kirsimeti.

Bayan da haɗin gwiwar jami’an tsaron jihar suka gano gawarsa da ta fara ruɓewa a daji kusa da gadar 2nd Niger, an binne shi makon da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da aka kama kuma aka nuna wa jama’a da ke da hannu a wannan lamari, wato Kevin Ikechukwu Ossai, wanda aka fi sani da Ikem, da wani da aka ambata da suna Ocha, sun tsere yayin da ‘yan sanda ke gudanar da wani samame don cafke wani da ake zargi da sayen motocin sata daga hannun gungun su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da tserewar su a wata sanarwa, inda ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dr Ikioye Orutugu, ya tura jami’an tsaro da kuma kayayyakin aiki don tabbatar da an sake cafke su.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ya bayar da umarnin gudanar da bincike da ɗaukar matakin ladabtarwa ga jami’an da suka nuna sakaci a wannan al’amari.

A lokacin wannan farmakin, ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wanda ake zargi da sayen motocin sata, tare da gano motoci biyu da ake zargin an sace daga hannun jama’a. Amma, abin takaici, waɗanda ake zargi biyu sun tsere daga wurin.

By ukarofi