Daga USMAN KAROFI
Shahararren mawaƙin Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, ya iso hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun da ke Eleweran, Abeokuta. Wannan ya biyo bayan miƙa kansa da ya yi a sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sanda (SCID) da ke Yaba, Legas, inda ya isa Abeokuta da misalin ƙarfe 1:23 na rana.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, CSP Omolola Odutola, ta bayyana cewa isowar Portable SCID na nuna fara gurfanar da shi a gaban shari’a dangane da binciken da ake yi kan wani hari da ake zargin ya kai wa jami’an gwamnatin Jihar Ogun.
Ta kuma tabbatar da cewa za a bi dukkan ƙa’idojin doka wajen shari’ar tare da bayar da cikakkun bayanai a kan lamarin a lokutan da suka dace.
Ta ƙara da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa yaɗa labaran da ba su da tushe.
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun, a cewarta, na nan daram wajen tabbatar da adalci da kuma tsaro a cikin al’umma.
