Daga USMAN KAROFI
Majalisar Dattawa ta gayyaci Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da manyan daraktocin Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), da Hukumar Leken Asirin Soja (DIA), domin su bayyana a gaban ta a bayan ƙofofi rufe. Ana son su yi bayani kan zargin da wani ɗan majalisar Amurka, Scott Perry, ya yi cewa Hukumar USAID tana tallafa wa ƴan ta’addan Boko Haram a Najeriya.
Duk da cewa majalisar dokokin Amurka na bincike kan wannan zargi, majalisar dattawan Najeriya ta yanke shawarar gudanar da nata binciken a zaman ta na ranar Laraba. Wannan batu ya samu kulawar majalisar ne bayan da Sanata Ali Ndume ya gabatar da ƙudiri kan lamarin, tare da goyon bayan wasu Sanatoci biyar.
Bayan muhawara kan ƙudirin, majalisar dattawan ta amince da kiran NSA da manyan daraktocin DSS, NIA, da DIA don yin bayani a sirrance. Za a sanar da su ranar da za su bayyana a gaban majalisar.
