Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da shirin kiwon awaki a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarin ta na bunƙasa tattalin arzikin al’ummar ta, gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da kiwon awaki a Katsina.

Mai ba gwamna shawara kan harkan dabbobi da gandun daji Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya bayyana wa manema labarai haka a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar.

Ya ce a tsarin kiwon gwamnati ne da kanta za ta ɗaukin nauyin kiwon da za ta fara da awaki guda 3000.

Suleiman Jibiya ya bayyana cewa gwamnati ta sami filin da zata gudanar da kiwon mai kadada 70 a garin larabawa a garin Katsina in da za a gudanar da kiwon.

Ya ce awakin da gwamnati ta saya akan kudin Naira biliyan 1.7 na daga cikin awakin da gwamnati ta saya guda 40.000 wanda tuni ta fara rabawa mata a faɗin jihar.

“An tanadi abincin su da magani tare da malaman kiwon lafiya da za su kula da su”inji Suleiman.

Ya bayyana manufar gwamnati akan wannan shiri da za ayi amfani da fasahar zamani wajen kiwon.

Mai ba gwamnan shawara ya cigaba da cewa da zaran sun fara haihuwa, ana sa ran raba su zuwa sassan jihar da haka zai bunƙasa tattalin arzikin al’ummar jihar baki ɗaya.

Mata goma a kowane mazaɓa 361 da ke faɗin jihar suka amfana da awaki guda huɗu kowanne su.

Su kuma mayan manoma guda goma kowanne su.

By ukarofi