Majalisar Malaman Kano ta sasanta rikicin Masallacin Sahaba

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ƙarshe dai Majalisar Malaman Jihar Kano ta cimma matsaya akan dambarwar Masallacin Jumma’a na Sahaba, dake Kundila a jihar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Majalisar, Sheikh Malam Ibrahim Khalil, wanda ya ce bayan zama da dukkanin ɓangarorin masallacin ne, majalisar ta yanke hukunci na ƙarshe akan rikicin.

Ya ce, sun yanke hukuncin cewa Sheikh Muhammad Bin Othman zai koma masallacin, yayin da Mai Kifi da sauran mutanensa kuwa za su cigaba da riƙe nasu masallacin na Jami’urrahman.

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaman da suka yi da manema labarai a Kano.

Ya ƙara da cewa, Sheikh Bn Othman ya amince zai cigaba da jagorantar sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba, yayin da ɗaya ɓangaren kuma zai cigaba da gudanar da harkokin masallacin Jami’urrahman.

Sannan, Malam Ibrahim Khalil ya yi godiya ga dukkanin jami’an tsaro musamman DSS saboda rawar da suka taka wajen tabbatuwar sulhun.

By Babaji