Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ýansandan Isra’ila sun kai samame wani kantin sayar da littattafai mallakin wasu Falasɗinawa da ke Gabashin Birnin Jerusalem, da Isra’ila ta mamaye, tare da kama masu kantin su biyu, abin da masu nazarin harkokin adabi, ýanjarida da masu nazarin zamantakewa ke kallo a matsayin zalunci ne da shigar da batun ilimi cikin harkar siyasa.
Mahmoud Muna da ɗan uwansa Ahmad, sun kasance a tsare a hannun ‘yansanda tun bayan kamun da aka yi musu ranar Lahadi da ta gabata, yayin da lauyansu Nasser Odeh, ke cewa ana tsare da su ne cikin wani mawuyacin yanayi da ke tattare da tsananin sanyi.
Ya ƙara da cewa, ýansandan na neman izinin kotu ta ba su damar ba da belinsu da cigaba da tsare su a gidajensu, ba tare da zuwa buɗe kantin da suke sayar da littattafai ba.
Mutanen dai suna harkar sayar da littattafai ne, a kantuna uku da suka mallaka, inda baƙi ýan ƙasashen waje, da manazarta ke zuwa yin sayayyar littattafai. Akasari suna sayar da littattafai ne, mujallu da jaridu, da takardun makaranta na yara, da waɗanda suka shafi nazarce-nazarce game da rikicin Isra’ila da Falasɗinu, a cikin harsuna daban-daban.
A cewar iyalin mutanen, ranar Lahadi ne jami’an tsaro cikin farin kaya suka far wa kantin da ke titin Salah ad-Din, babu wata sanarwa ko gargaɗi, inda suka riƙa cire duk wani littafi da aka rubuta sunan Falasɗinu, ko tutar ƙasar Falasɗinu mai launin ja, kore da fari.
Daga cikin littattafan da aka kwashe har da wani sabon littafin da aka fitar kwanan nan da ke bayani game da rikicin Gaza, da kuma wani littafin yara da aka saka launi a jiki, wanda ke ba da labarin mamayar da Isra’ila ta ke yi wa al’ummar ƙasar Falasɗinu.
Rundunar ‘yansandan Isra’ila cikin wata sanarwa da suka sun ce, “an kama mutanen ne saboda suna sayar da littattafan da za su tunzura mutane da sanya su shiga ta’addanci.”
Rahotanni daga wata majiya na bayyana cewa, bayan awoyi shida da tsare masu kantin, ýansanda sun janye zargin ta’addanci da suke yi musu, amma sun cigaba da tuhumarsu kan zargin ƙoƙarin tayar da hankalin jama’a.
Ana zargin wannan sabon cin zarafin da muzgunawa harkar littattafai da marubuta, ba ya rasa nasaba da hirar da wata jarida ta buga a game da sabon littafin da Nathan Thrall, wani ba’amurke da ya taɓa cin gasar marubuta ta duniya ta Pulitzer, ya rubuta akan mamayar da Isra’ila ke yi wa Falasɗinu mai taken, ‘Wata rana a rayuwar Abed Salama: Nazari kan zaluncin da ke faruwa a Jerusalem.
Akwai alamun ýansandan za su cigaba da kai wannan samame da suka ce suna kai wa ne domin shawo kan yadda ake amfani da da rubuce-rubuce wajen jefa rayuwar Yahudawa cikin haɗari, ta hanyar yaɗa ƙiyayyar Isra’ila a zukatan masu karatu, ciki har da ƙananan yara masu tasowa.
An rubuta a shafin rundunar ‘yansanda na manhajar ɗ cewa, an samu wani littafin yara da ake shafawa launuka mai suna’ Daga Kogi Zuwa Teku’ (From the Riɓer to the Sea), an rubuta wasu kalamai da ke nuna goyon baya ga ayyukan ta’addanci.
Marubuta da masu nazari harkokin talifi da littattafai sun yi tir da wannan halayya ta jami’an tsaron Isra’ila da suka ce babbar barazana ce ga cigaban ilimi a duniya.
Marubucin littafin yaran, ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Nathi Ngubane, ya bayyana damuwa game da yadda Isra’ila ke fakewa da littafinsa don cigaba da zaluntar Falasɗinawa.
“Manufar littafinmu shi ne mu ilimantar da yaran Afirka ta Kudu da duniya bakiɗaya kan irin rayuwar da Falasɗinawa ke ciki, gwagwarmayar da mutanen Falasɗinu ke yi ta neman ýancinsu da mamayar Isra’ila. Ba don tunzura mutane ko haddasa rikici ba, sai don neman adalci. “
Wannan ba shi ne karon farko da jami’an tsaro ke hana sayar da wannan tallafin yara ba, don ko a shekarar da ta gabata ma sai da aka yi irin haka, bayan da wata ƙungiyar Yahudawa mazauna Afirka ta Kudu ta nemi a hana buga littafin.
Idan za a iya tunawa, ƙasar Afirka ta Kudu ta kai ƙarar ƙasar Isra’ila Babbar Kotun Duniya ta ICJ, dangane da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza, inda ta hallaka fiye da rayuka 36,500, akasarin su fararen hula.
