Littafin ‘Wasa Da Rayuwa’: Ya bankaɗo tushen ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Duk wanda Allah Ya nufa da samun damar karanta littafin ‘Wasa Da Rayuwa’ wanda Zainab Abdullahi Musa, da aka fi sani da Lailat Abdullahi, ta rubuta, kuma littafin da ya zama na uku a Gasar Tsangayar Gusau na shekarar 2024, zai fahimci lallai ana samun cigaba sosai a harkar rubutun adabi na Hausa. Sannan su kansu matasan marubuta na yanzu, musamman waɗanda suka fara rubutu a zamanin rubutun onlayin, suna ƙara samun gogewa da sanin dabarun rubutun labari, wanda zai zama abin misali a ko’ina a duniya. 

‘Wasa Da Rayuwa’, littafi ne da ke ɗauke da labarin wata karkara ko ƙauye a ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya, wadda ke fuskantar ƙalubalen tsaro da hare-haren ýan bindiga, sakamakon rincaɓewar saɓanin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya. A dalilin yawan kai ruwa rana da ake yi a wannan yanki, lalacewar al’amura har ta kai ana ɗaukar makami, ana garkuwa da mata da raunana, don karɓar kuɗin fansa ko biyan wata buƙata. An durƙusar da harkokin noma sai da amincewar ýan bindiga, zamantakewa ta taɓarɓare, tarbiyyar matasa ta lalace, harkar lafiya ta gurgunce, rayuwa ta zama cikin tsoro da fargaba. 

Marubuciyar wannan littafi wacce matashiya ce da ba ta wuce shekaru 26 ba, ta yi ƙoƙari sosai wajen nazarin halin da yankin da ta fito na Jihar Katsina yake ciki, tare da samar da shawarwari na yadda za a kawo gyara da inganta tsaro da zaman lafiya. Muhimmancin kula da kyautata tarbiyya, da kiyaye haƙƙokin iyali, illolin ɗora wa yara mata talla, da kuma tasirin samar da shugabanci nagari.

A tsakanin shafuka 72, littafin ya koyar da mai karatu darussa da dama, da suka shafi muhimmancin haɗa hannu don taimaka wa gwamnati da jami’an tsaro wajen samar da tsaro a cikin al’umma, gudunmawar ýan jarida wajen samar da ingantattun labarai da rahotanni na yadda za a bankaɗo wasu munana ayyuka da ake aikatawa a ɓoye ba tare da sanin jami’an tsaro ko hukumomi ba. Da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da ya zama ruwan dare a zaurukan sada zumunta, abin da ke karkatar da hankalin jama’a daga gaskiyar abubuwan da ke faruwa. 

An gina labarin littafin ne akan wani matashin ɗan jarida, mai koyon sanin makamar aiki, mai suna Abdallah wanda ya ƙudurta niyyar shiga wani gari da ake kira ɗankurna, domin gudanar da bincike kan halin taɓarɓarewar tsaro da yankin ke ciki, da nufin fitar da gaskiyar labarin abubuwan da ke faruwa ga duniya. A hanyar su ta shiga ƙauyen tare da abokinsa Muhammad Sani sun ci karo da wasu matasa da ke yunƙurin yi wa wata yarinya fyaɗe a cikin wani kango, inda ba da ɓata lokaci ba shi ɗan jaridar ya taimaka wajen kuɓutar da ita. Wannan yarinya da ta kasance tauraruwar labarin ta farko Fatima Binta tare da shi Abdallah tauraron na biyu da abokinsa, sun shiga cikin ƙauyen ɗankurna tare, yayin da suka samu masauki a gidan Maigari. Wannan shi ne tushen labarin, da yadda Abdallah ya yi wasa da rayuwar sa, wajen shiga binciken labarin ýan bindiga da halin da jama’ar ɗankurna ke ciki. A dalilin haka labarinsa ya kai har kunnen wani madugun ýan bindiga mai suna ɗan’agundi, da ke da sansaninsa a daji, wanda ya aika aka ɗauko masa Abdallah, don ya ji abin da ya sa yake bincike kan abubuwan da suke yi. 

Babu shakka wannan littafi ya tsaru da kyau, an yi amfani da basira da hikima ta ƙirkira wajen gina labarin cikin shafukan da ba su wuce 72 ba, kuma an yi amfani da ingantacciyar Hausa da kiyaye ƙa’idojin rubutu. Duk da yake dai akwai tasirin Hausar Katsinanci a ciki, da kuma kurakurai wajen haɗa wasu kalmomi ko rabawa a inda ya dace. Amma duk da haka littafin ya ƙayatar sosai, don zai iya samun taurari bakwai cikin goma, saboda ya cancanta.

Babu mamaki shi ya sa littafin ya shiga cikin jerin littattafan Hausa goma da Sashin Hausa na BBC ya yi hasashen za su samu karɓuwa a wajen masu karatu cikin wannan shekara. Wannan ma babbar nasara ce da littafin ya samu, bayan zaman sa na uku a cikin littattafan da suka yi nasara a Gasar Marubuta ta Gusau Institute a shekarar 2024. 

Kamar yadda na nuna a baya, littafin an gina shi ne kan tushen ƙalubalen tsaro da yankin arewa maso yammacin Nijeriya ke fuskanta. Sannan kuma akwai wasu ƙananan jigogi da za mu iya cewa sun taka rawa cikin labarin, da suka haɗa da illolin shaye-shaye, illolin tallace-tallace, illar rashin kulawar shugabanni da ýan siyasa kan halin da jama’ar da ke zaune a ƙauyuka ke ciki, illar rashin nuna adalci a tsakanin iyali, amfanin ilimin addini da na zamani, da kuma illolin yaɗa labaran ƙarya a zaurukan sada zumunta. 

A ɓangaren kurakurai kuwa, nan ma akwai wasu abubuwa da na yi la’akari da su a labarin. Na farko dai littafin ba a rubuta shi cikin tsarin babi-babi ba, don haka ba a yi masa mabuɗi da murfi ba. Sannan an fara buɗe labarin da salon ciki, ba a yi nisa ba kuma sai aka sauya salon zuwa na waje, ba tare da wani bayani ba, ko a nuna dama a tunani ba ne. Harwayau, a yayin da tauraruwar labarin ke bai wa Abdallah labarin rayuwarta, ba a bayyana mana inda suka haɗu ba ko kuma abin da ya haifar da hirar ta su. Mai karatu zai tsinci hirar ne kawai daga sama, wanda ke nufin akwai wani abu da aka rasa a wajen, da zai taimaka wajen ɗinke labarin baya, daga inda Abdallah yake dawowa daga bayan gari inda ya je yi wa iyayensa waya, saboda rashin layin sadarwa. 

Idan ka cire waɗannan, za ka fahimci lallai wannan littafi ya ciri tuta matuƙa, kuma ya zama kamar wani daftari da hukumomin tsaro da gwamnati za su yi amfani da shi wajen nazarin halin da al’ummar yankin Arewa Maso Yamma ke ciki a hannun ýan bindiga, da rashin samun kulawar hukumomi. 

Lallai Zainab Abdullahi Musa ta cancanci yabo, kuma ya kamata a ƙarfafa mata gwiwa sosai, da sauran abokan rubutunta masu irin wannan basira ta ƙirkiro da labari, don cigaban al’umma, ta cikin hikima da hazaƙa.

By ukarofi