
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da barikin Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a Yola, Jihar Adamawa, wanda kuma shi ne na farko a Nijeriya.
Shugaban NDLEA, Mohamed Buba Marwa (rtd), ya ce barikin zai taimaka wajen bunƙasa ayyukan jami’ansu wajen yaƙin da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.
Ya ce, rashin bariki a baya ya sanya jami’an hukumar da iyalansu faɗawa cikin haɗurra.
An buɗe barikin ne, wanda ke unguwar Kwanan Waya, da ke da faɗin Hekta 18 ga jami’an NDLEA da iyalansu, wanda kuma aciki akwai ofsoshi, gidajen jami’a da wuraren nazarin ayyuka da za su inganta jami’an.
Da ya ke jawabi, Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyana aikin a matsayin babbar hanyar inganta ɗan-adam, ya na mai bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na inganta wuraren ayyukan jami’an NDLEA.
Ya kuma yi kira a gare su da su kasance masu tsare ayyukansu bisa ƙwarewa.
Haka kuma ya yaba wa NDLEA bisa ƙoƙarinta na daƙile ayyukan sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wanda hakan ɗaya ne daga cikin matakan samar wa Nijeriya gobe mai kyau.
Gwmanan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce aikin zai taimaka wajen samar da yanayi na haɗaka mai inganci ga ayyukan jami’an don kare goben Nijeriya daga miyagun ƙwayoyi.
