
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Amurka, Donald Trump ya a bada umarnin a gudanar da bincike game da yadda aka sarrafa kuɗaɗen da aka ware wa Nijeriya da wasu ƙasashe.
Kamar yadda aka wallafa a shafin X na Ayyukan Amurka ga Nijeriya a ranar Talata, an samar da gamsassun hanyoyin nazari da za su taimaka wajen tantance kuɗaɗen tallafin Amurka sun isa ga waɗanda aka ware saboda su.
Ta ce, Amurka ta yi alla-wadai da addabar rayukan al’umma da ƙungiyar Boko Haram da wasu ƙungiyoyi ke yi a Nijeriya.
Binciken zai taimaka wajen tabbatar da sarrafa kuɗaɗen bisa ka’ida da kuma dacewa da tsarin manufofin harkokin wajen Amurka.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani ɗan majalisa a Amurka mai suna Scott Perry ya yi zargin USAID da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addancin ƙungiyoyin Boko Haram, ISWAP, ISIS, Al-Qaeda da makamantansu.
