Gafakan Akko ya buƙaci garambawul a siyasa don inganta Najeriya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Dakta Auwal Abdullahi, Gafakan Akko, ya bayyana buƙatar gaggawa na sauyin aƙidu da tsare-tsare a harkar siyasa a Najeriya, yana mai cewa hakan ne kawai zai tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya da zaman lafiya mai ma’ana.

Da yake magana a wata hira da ya yi da manema labarai a Gombe, Gafaka ya jaddada cewa lokaci ya yi da siyasa za ta fita daga tunanin son zuciya zuwa tsarin da ya mayar da hankali kan gaskiya da ci gaban ƙasa.

“Idan har jam’iyyun siyasa ba su samu ƙarfi daga aƙidu masu inganci ba, ba za su iya bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya ko kuma hada kan al’ummomin ƙasar nan ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa rashin shugabanci mai inganci da tsare-tsare nagari shi ne tushen matsalolin da suka dabaibaye ƙasar. “Dole ne shugabanni su kasance masu cancanta da ƙwarewa, ba wai ana naɗa su bisa son zuciya ko wasu tsare-tsare na musamman ba. Wannan ne kawai zai tabbatar da cewa muradun ƙasa sun fi samun fifiko,” ya ce.

Gafaka ya yi kira ga garambawul a harkokin siyasa, yana mai bayyana cewa dole ne a canja tunani da dabarun siyasa domin a samu cigaban ƙasa. Ya ce, “Abin da zai kawo ci gaba shi ne tunanin haɗin kai da girmama haƙƙin kowa da kowa.”

Har ila yau, ya buƙaci shugabannin siyasa da su rungumi manufofi masu inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar ƙasa, domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da cigaban Najeriya.

A cewarsa, jam’iyyun siyasa na da rawar gani wajen gina aƙidu masu kyau ga mambobinsu, wanda hakan zai haifar da shugabanni masu kishin ƙasa da ƙwazon aiki. Ya ce, “Ɗabi’un gaskiya da adalci su ne ginshiƙin Najeriya mai kyau da arziki.”

Ya kammala da yin kira ga ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su haɗa kai don ganin an samu sauyi a siyasa da kuma tabbatar da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi