Karɓe ikon ƙananan hukumomi cin amanar ƙasa ne – Gargaɗin Ministan Shari’a ga gwamnoni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyana karɓe iko ba bisa doka ba na ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi a matsayin cin amanar ƙasa.

Antonin ya faɗi hakan ne a yayin wani taro da Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta shirya a Abuja, ranar Laraba.

Fagbemi, wanda Daraktan ofishin ɗaukaka ƙara na Ma’aikatar Shari’a, Tijani Gazali ya wakilce shi, ya ce duk da hukuncin Kotun Ƙoli na ba su ƴancin cin gashin kai da dokokin da ke hana shiga harkokinsu, wasu gwamnoni da majalisun dokokinsu suna cigaba da juya lamuran zaɓaɓɓun ciyamomi ba bisa doka ba.

Ya kuma zargi kwamishinonin Shari’a na jihohi da rashin bai wa gwamnoninsu shawarwarin doka, ya na mai gargaɗin hukunta duk wani gwamna da aka samu da hannu a aikata irin wannan laifin.

By Babaji