Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Katsina kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso yamma, Dikko Umaru Raɗɗa, ya yaba wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da majalisun Nijeriya kan samar da hukumar raya yankin Arewa maso yamma yana mai bayyana hakan a matsayin babban hanyar samar da cigaba ga yankin.
A yayin da yake jawabi a lokacin da hukumar ta kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar, Raɗɗa ya jaddada muhimmancin hukumar.
“Wanann hukuma ce mai muhimmanci da ya kamata mu ci moriyarta yadda ya kamata. Samar da hukumar da naɗa minista daga wannan yankin ya nuna irin yadda gwamnati ta himmatu wajen magance matsalolin da ke damun yankin,” a cewarsa.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin tsaro a matsayin muhimmin abu na farko tare da yaba wa irin cigaban da aka samu.
“Tsaro muhimmin abu ne. Kuma muna yaba wa al’umma ƙoƙarin da rundunar sojin Nijeriya da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren tsaro. Ana cigaba da samun tsaro, kuma mun himmatu wajen kawo ƙarshen wannan matsala,” Radda ya faɗa.
A ƙoƙarin magance matsalolin yankin, gwamnan ya jaddada muhimmancin bunƙasa noma da ilimi. “ƙarfin tattalin arziƙin Arewa maso yamma ya ta’allaƙa ne da noma,” ya bayyana.
Raɗɗa ya kuma bayyana wasu shirye-shirye da yake yi a ɓangaren ilimi da ya haɗa da “gina ƙananun makarantun sakandare guda 150,” wanda ya nuna irin yadda ake samun cigaba a ɓangaren ilimi.”
Ya yi kira da a rarraba tallafi yadda ya kamata a yankin ta la’akari da irin buƙatun kowacce jiha.
“Muna fatan hukumar za ta yi la’akari da yawan jama’a da girman jiha da irin ƙalubalen da kowacce jiha ke fama da ita wajen ba da tallafi.”
Ya kuma nuna muhimmancin haɗin guiwa a tsakanin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma tasirin wannan hukumar.”
Gwamnan Raɗɗa ya kuma yi alƙawarin haɗa kan gwamnonin yankin Arewa maso yamma inda ya ce, “Kanmu a matsayin shugabanni a haɗe yake kuma za jingine kowanne irin bambanci wajen inganta tattalin arziƙin yankin. Za mu ba wa wannan hukuma dukkan goyon bayan da take buƙata tare da alƙawarin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da juna wajen samar da cigaba.”
Shi ma a nasa ɓangaren, sanata Muntari ɗandutse, mai wakiltar Katsina ta Kudu, ya yaba wa hukumar raya yankin Arewa maso yamma wajen samar da cigaba a yankin.
“Mun daɗe muna kira kan samar da wani tsari na magance matsalolin wannan yanki kuma a yau ga shi mun ga sakamakon wannan ƙoƙari da muka yi,” inji sanatan.
Shi ma Sanata Dandutse ya yaba wa Shugaba Tinubu na samar da wannan hukuma yana mai cewa “samar da hukumar nan babban mataki ne na tabbatar da cigaba a kowanne yanki da tsara irin cigaban da muke da buƙata.
“Akwai buƙatar mu fara shirin sake tsugunar da waɗanda rashin tsaro ya raba da gidajensu. Da yawa sun rasa gidajensu da gonakinsu kuma suna buƙatar taimakonmu domin su cigaba da rayuwa.”
Sanatan ya nuna ƙarfin guiwarsa kan shugabancin Raɗɗa a matsayin shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma na farko da kuma tabbacin da yake da ita cewa haɗin kan da aka samu zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin da ake fama da ita a yankin.
Shi kuma a nasa ɓangaren, shugaban hukumar raya yankin Arewa maso yamma, Lawal Samaila Abdullah Yakawada, ya jaddada muhimmancin samar da doka da za ta tabbatar da ayyukan hukumar.
Ya ce an tsara hukumar ne domin tabbatar da ayyukan da ya kamata a ce an yi su don cigaban al’umma sun yi su. Sannan ya nuna ƙarfin gwiwarsa kan shugabancin Raɗɗa wajen jan ragamar ƙungiyar gwamnoni domin ciyar da yankin gaba.
