Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da wani biki a hukumance don raba tan 100 (kg 100,000) na dabino ga Nijeriya a wani bangare na ayyukan agajin jin kai da take yi duk shekara.
Shirin wanda cibiyar ba da agajin jin kai da taimakon jin kai ta Sarki Salman (KSrelief) ta ɗauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafawa iyalai masu rauni a fadin kasar da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.
A yayin taron, jakadan mai kula da masallatai biyu masu alfarma a Nijeriya Faisal bin Ibrahim, ya miƙa ƙwazon masarautar kan ayyukan jinƙai.
Ya bayyana matukar godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al’ummomi marasa galihu a faɗin duniya.
Al-Ghamdi ya bayyana cewa rabon na bana ya hada da tan 50 na dabino da za a raba a Abuja da kuma wani tan 50 shi kuma a Kano, wanda ya ce hakan ana tinsa ne domin tallafi da Saudiyya ke badawa domin kasashe kamar su Nijeriya.
Al-Ghamdi ya jaddada aniyar Masarautar na karfafa hadin gwiwa da Nijeriya a bangarori da dama, musamman a harkokin jin kai da na Musulunci.
