Azabtar da matashi: Matasa sun ƙona ofishin ‘yan sanda a Ondo

Spread the love

Wasu matasa da suka fusata sun ƙona wani ofishin ’yan sanda a garin Ifon na ƙaramar hukumar Ose da ke Jihar Ondo.

Wannan ya faru ne sakamakon mutuwar wani matashi, wanda aka yi zargin cewa ‘yan sanda sun gana mishi azaba a lokacin da suke tsare da shi.

Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, amma har zuwa yau Lahadi ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba.

An samu bayanai daga garin da ke da iyaka da jihar Edo cewa mutuwar matashin ta harzuƙa abokan yaron da sauran jama’ar garin suka shiga zanga-zangar da ta kai ga ƙona ofishin ‘yan sandan.

ɗaya daga cikin waɗanda suka bada bayani kan lamarin ya ce lamarin ya faru ne a dalilin bikin Ranar Masoya ta Duniya da aka yi, ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da aukuwar lamarin ta kuma ce kwamishinan ‘yan sandan jihar na kan hanyarsa ta zuwa garin domin kwantar da hankali.

By ukarofi