Rahoton Oronsaye: Tinubu ya fasa haɗe NCAA da NAMA – Keyamo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya janye batun haɗewar Hukumar Kula da Zurga-zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) da Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya (NAMA), kamar yadda rahoton Steɓe Oronsaye ya bada shawara.

Ya kuma bayyana cewa, an cire masana’antar sufurin jiragen sama daga haramcin balaguron da aka sanya wa jami’an gwamnatin tarayya a shekarar da ta gabata.

Idan za a iya tunawa, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da dakatarwar da jami’an gwamnati yawan balaguro zuwa ƙasashe waje wanda ya fara aiki daga watan Afrilun bara.

Keyamo ya bayyana cewa an cire ɓangaren sufurin jiragen sama daga haramcin ne saboda shugaba Tinubu na da muradin samun sauyi da ci gaba a fannin.

An sanya haramcin ne biyo bayan tashin farashin tafiye-tafiye da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka yi.

Sanarwar da aka fitar a bara ta bayyana cewa: “Bisa la’akari da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu da kuma buƙatar gudanar da kasafin kuɗi, na rubuta ne domin in sanar da umarnin shugaban ƙasa na sanya takunkumi na wucin gadi kan duk wani tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa da jama’a ke ba da tallafi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a dukkan matakai, na tsawon watanni uku daga 1 ga Afrilu 2024.

“Duk jami’an gwamnati da suke da niyyar zuwa duk wata balaguron balaguron kasa da kasa da jama’a za su bayar, dole ne su nemi izinin shugaban ƙasa aƙalla makonni biyu kafin su fara irin wannan balaguron, wanda ya zama dole.”

Ministan ya bayyana dalilan da suka sa aka cire su a Abuja a wajen bikin cika shekaru 25 da kafa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya NCAA.

Dangane da haɗewar NCAA da NAMA, ya ce: “Tun daga farkon farawa, mun ga sauye-sauye masu ban mamaki a cikin sassanmu, kama daga ingantattun matakan kulawa da tsara manufofi, tsaro, tsauraran dokoki da ƙa’idoji, ci gaba a cikin sarrafa zirga-zirgar jiragen sama da takardun shaida na filayen jirgin sama.

By ukarofi