Yadda Tinubu ya canza ra’ayinsa kan naɗina a matsayin minista – El-Rufai

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa ba majalisar dattawa bace ta ƙi amincewa da shi a matsayin minista, kamar yadda wasu ke yayatawa. A wata hira da aka yi da shi a Arise TV, ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ne kawai ya canza shawara kan naɗinsa.

El-Rufa’i ya bayyana cewa bayan kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a Kaduna, ya shirya shirin kansa, amma Tinubu ya buƙace shi da ya dakatar da shirin don ya zama minista. Ya ce sun cimma matsaya amma daga baya ko dai shugaban ƙasa ya canza shawara ko kuma wani abu ya faru, amma a cewarsa, ba shi da wata damuwa game da hakan.

A watan Agustan 2023, majalisar dattawa ta dakatar da tabbatar da shi a matsayin minista, tana mai danganta hakan da rahoton tsaro daga Hukumar Tsaron Ƙasa (SSS). Sai dai El-Rufa’i ya musanta cewa majalisar ce ta hana shi, yana mai jaddada cewa Tinubu ne kawai ya fasa saka shi a majalisar ministocinsa.

By ukarofi