
Daga BELLO A. BABAJI
Hajiya Hauwa Yakub Usman, wadda sirika ce ga Ministan Labarai da Wayar kan al’umma, Mohammed Idris, ta rasu tana da shekaru 70 a duniya.
An yi mata sallar jana’iza ne a babban masallacin ƙasa, wato National Mosque dake Abuja, inda kuma aka binne ta a maƙabartar unguwar Gudu a birnin.
Manyan jami’an gwamnati ne suka halarci jana’izarta waɗanda suka haɗa da Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu; Ministan Kasafi da Shirya Tattali, Sanata Atiku Bagudu; da wasu daga cikin jami’an Ma’aikatar Labarai da daraktocin hukumomin gwamnati da dai sauransu.
Marigayiyar ta rayu ne da ƴaƴa da kuma jikoki.
