Ana dab da yin sabon ƙidaya a Nijeriya bayan Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ana cigaba da shirye-shirye na fara gudanar da sabon ƙidaya a Nijeriya tun da aka yi na ƙarshen a watan Nuwamban shekarar 2006.

A yayin ganawa da jami’an Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai kafa kwamiti ne da zai haɗa kasafin ƙidayar da yanayin tattalin arziƙin ƙasa don su dace wajen tafiyar da aikin.

Ya ce, daga cikin tsare-tsaren akwai sanya Hukumar Katin Ɗan ƙasa (NIMC) a matsayin ɗaya cikin ɓangarorin da za su bada gudunmawa wajen gudanar da aikin.

Ya kuma jaddada ƙoƙarinsa na tabbatar da an samu haƙiƙanin adadin mutanen Nijeriya a ƙidayar, wanda hakan zai taimaka wajen tsara yanayin samar da ci-gaba ga al’ummar Nijeriya a matakai daban-daban.

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, shirye-shiryen gwamnati ba za su cimma nasara yadda ake buƙata ba ba tare sanin haƙiƙanin adadin al’umma ba, ya na mai bada misali da shirin sayarwa da raba taki ga al’umma.

Ya kuma buƙaci tawagar NPC’n da ta sanya tsarin tantancewar ya zama bai-ɗaya ta yadda za a samu hanyoyi daban-daban waɗanda suka haɗa da ɗaukar hoton fuska da muryar mutum.

A nasa jawabin, Shugaban NPC, Nasir Isa Kwarra, ya ce kasancewar kimanin shekaru 19 da suka gabata aka gudanar da ƙidayar ƙarshe a Nijeriya, hakan yasa ba a iya amfani da adadin wancan lokacin wajen gudanar tsare-tsare musamman waɗanda suka shafi adadin al’umma kai-tsaye.

By Babaji