Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta buƙaci a ci gaba da amfani da kaso 7.5% na VAT a ƙudirin gyaran dokokin haraji da ake shirin aiwatarwa. A cewar ƙungiyar, hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa matsin tattalin arziki ga ‘yan kasuwa da talakawa.
A cikin rahoton da sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba, ya sanyawa hannu, ACF ta jaddada buƙatar inganta hanyoyin tattara haraji, ƙara yawan masu biyan haraji, da kuma amfani da fasahar zamani don haɓaka kuɗaɗen shiga. Haka nan, ƙungiyar ta buƙaci a cire haraji daga kayan aikin noma da kuma gyara wasu kalmomin dokar haraji.
Har ila yau, ACF ta buƙaci a rage ƙarfin iko da aka bai wa shugaban hukumar haraji da majalisar gudanarwa, tare da samar da sabbin daraktoci shida daga kowanne yanki na ƙasa. Kungiyar ta buƙaci ‘yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki su ci gaba da tattauna ƙudirin gyaran dokokin haraji don tabbatar da adalci ga kowa.
