Ayyukana su ne a gabana, ba mayar da martani ba – Ribaɗu ga El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya ƙaryata kalaman tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, na cewa yana shirin ɓata masa suna saboda burinsa (Ribaɗu) na tsayawa takara a zaɓen shekarar 2031.

A wata hira da aka yi da El-Rufa’i ta gidan telebijin na Arise a ranar Litinin, ya zargi Ribaɗu da haɗa kai da Gwamna Uba Sani na Kaduna da Hukumar Hana Rashawa da Laifuka masu Kama da ita (ICPC) don ɓata masa suna a idon al’umma.

Saidai, a wata takarda daga ofishin Ribaɗu da aka fitar a ranar Litinin, NSA’n ya ce bai haɗa kai da kowa ba don muzanta wa El-Rufa’i ta kowacce fuska.

Ya kuma ce, bai taɓa tattauanawa da wani ba game da tsayawa takara a 2031, ya na mai cewa duk ƙoƙarin da ya ke yi shi ne ganin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi nasara da kuma ciyar da Nijeriya gaba.

Don haka ne ya yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa kalaman na El-Rufa’i akansa, ya na mai cewa ayyukan ofishinsa ya ke ƙoƙarin ji da su ba cacar baki da wani a mediya ba.

By Babaji