Mun sha zama da majalisar dokoki kan ilimin mata – Nafisa Halliru

Spread the love

“Tun 2012 zuwa yau nake ba wa gwamnatin Jigawa gudunmawa wajan cigaban ilimi”

Daga UMAR AKILU MAJERE

Hajiya Nafisa Halliru Haruna wata fitacciyar ýar gwagwarmayar ƙungiyoyi ce da sunanta ya jima a harkar Jihar Jigawa akan harkokin ilimi da kiwon lafiya.

Hajiya Nafisa tana ɗaya daga cikin mata da suka sadaukar da rayuwarsu domin cigaban al’umma musamman wajan ganin ta sanya ‘ya’ya mata sun shiga andama wajan samun ilimin boko da na zamani.

Nasani mai karatu zai so ya ji tarihin hajiya Nafisa da jin asalinta ko daga ina ta fito?

Hajiya Nafisa Halliru an haife ta a garin Birnin Kano a unguwar Yakasai da ke cikin Birnin Kano a Arewacin Najeriya.

Ta yi makarantar primary a Kano, sakandire a Bauchi. Ta yi karatun diploma a kwalejin kimiyya da fasaha ta Jihar Kano, wato Kano poly. Ta wuce kwalejin kimiyya da fasaha ta AkwaIbom inda annan ta yi karatun babbar diploma, wato HND, kuma ta yi ‘masters in Deɓelopment studies’ a FUD bayan ta kammala ne, ta yi aure acaan Auchi. Daga baya ne aurenta ya mutu ta dawo Kano da zama.

Dayake tana da wata ýar uwarta ma’aikaciyar NTA a nan Jigawa, Hajiya Hauwa Halliru takan ziyarce ta lokaci-lokaci daga ƙarshe sai ta ji tana da sha’awar dawowa wajanta da zama. Shine a lokacin mulkin Lamido ta dawo aka bata aikin baturen zaɓe bayan an kammala zaɓe shine sai ta ga Birnin Dutse yanada daɗin zama babu hayaniya babu tashin hankali kuma ana samun wuta akan lokaci shine ta nemi sahalewar mahaifanta zata dawo wajan yayarta ta zauna ,kuma suka amince mata ta dawo.

Bayan wani lokaci ne ta tsunduma cikin harkar ƙungiyoyi wanda shine haryanzu take ciki anan suka haɗu da mijinta na biyu marigayi Baffa Nayaya wadda shi ma ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Duk da cewar Hajiya Nafisa abinda ta karanta a jami’a lokacin da ta yi diploma da HND akan ‘accountancy’ ba ta taɓa tunanin zatayi aikin gwamnati ba. Babban burinta shi ne, ta samu wata dama da zata taimaka wa al’umma. Kwatsam sai ta tsinci kanta a cikin harkar ƙungiyoyi, wato ‘ciɓil society’.

Ta kasance mace mai tausayi da ƙoƙarin neman na kanta, ta kasance mai hazaƙa akan duk abinda ta sanya a gaba, ta zabi ta zauna a Dutse a unguwar Galadanci saboda yanayin Jihar Jigawa na zaman lafiya kuma Birnin Dutse ya kasance birni marar cinkosan jama’a, kuma

 akwai ƙarancin tashin hankali, gari ne da babu hayaniya kuma waje ne da ake samun hasken wutar lantarki akai akai babu kakkautawa.

Wakilinmu na Jihar Jigawa Umar Akilu Majeri ya sami ganawa da Hajiya Nafisa, ya zanta da ita a ƙofar gidanta da ke unguwar Galadanci.

Wakin namu ya fara yi mata tambayoyi kamar haka;

MANHAJA: Mai karatu zai so yasan wacce ce ke?

HAJIYA NAFISA: Sunana Hajiya Nafisa Halliru Haruna.

Batun tarihin rayuwarki?

An haife ni a Jihar Kano a unguwar Yakasai da ke tsakiyar Birnin Kano. Mahaifina Alhaji Halliru ma’aikacin kwastam ne. Na yi makarantar primary a Kano, na yi sakandire a auchi, na wuce Kano poly inda na yi diploma a ɓangaren akawu, na wuce Akwai ibom polytechnic na sake yin karatun babbar diploma akan aikin akawu.

Na yi aure har sau biyu, mijina na farko Allah ya kawo rabuwarmu bayan wasu shekaru, na sake aure anan Jigawa shi kuma mijina Allah ya yi masa rasuwa sakamakon ciwon daji, Malam Baffa na Yaya. Allah ya gafarta masa 

Ban taɓa haihuwa ba, bani da ‘ya’ya, yau kusan shekaru goma sha huɗu na yi a Jigawa, kuma shekaru takwas ina zaune a gidana na unguwar Galadanci, inda na yi zaman aure bisa amincewar mahaifina. Wannan shi ne tarihina a taƙaice.

Hajiya yaya za ki kwatanta karfin ƙungiyarku ta SAɓI ?

A gaskiya ƙungiyar ta yi, domin mun yi amfani da ƙungiya wajan cimma burin da muke da shi mun yi amfani da horon da ƙungiya ta bamu wajan aiki da gwamnati don cigaban al’umma.

Bazan manta ba awani taro shugaban ƙungiyar saɓi na wancan lokaci Malam Jibril Ali Giginyu ya ba mu damar kowa ya zaɓi ɓangaren da yake ganin zai iya bada gudunmawa. Ni a lokacin sai na zaɓi ɓangaren PTE, wato ‘Partnership for Transforming Education’, saboda ni ina son duk abinda ya shafi samun illimi da na addini da na boko, saboda irin gudunmawar da na bayar a ɓangaren da kuma irin rawar da na taka wajan faɗakarwa da nunawa iyaye anfanin ilimin ‘ya mace da yadda aka dinga sa yara mata a makarantar boko a garuruwan da muka yi faɗakarwa kusan babu wani ɗan jarida, ko wani ɗan ƙungiya da bai sanni ba ko a ma’aikatar ilimi a Jihar Jigawa.

Zan so ki gaya min ko menene aikin ƙungiya?

Shi aikin ƙungiya shi ne na farko mutun ya samu illimi akan fannin da yake son yin aikin, wato ilimin ko lafiya ko ‘gender’.

a samu masu ɗaukar nauyin ƙungiya ko daga nan cikin gida ko ƙasashen waje domin ba a yin aikin ƙungiya da ka, dole dai da masana waɗanda za su ba ka horo, misali, ‘concept of adɓocacy’, ‘concept of ɓolunteerism’, ‘gender and social inclusion’, da sauransu.

Da horon da muka samu muka dinga yin ‘adɓocacy on policy for free girl child education’. Mu ne muka kawo shi a lokacin gwamnatin Lamido domin mun taso mun ga yara mata sun samu ilimin zamani da na addini yadda wasu mata a duniya suka zama, saboda ilimi da irin gudunmawar da suka bayar wajan cigaban ilimin yara mata a ƙasashen su.

Hakama mun yi ‘adɓocacy da Esspin’ akan harkokin ilimin yara mata saboda mahinmancinsa badan komai ba sai don akwai buƙatar mu ga an taimaka wa ‘ya’ya mata, mutane da yawa sun mara mana baya a lokacin musamman ma’aikatar ilimi da sarakuna da sauran jama’a masu kishin ilimin ‘ya’ya mata .

Mun yi zama da ‘yan Majalissar Dokoki akan ilimin yara mata akan kowanne ɓangare kuma wajen da za mu bada shawara ayi gyara, mun bayar, wajan da ake da buƙatar gyara mun bada shawara an gyara .

Mun bada gudunmawa wajan kasafin kuɗi da gwamnati ke yi a duk shekara gun da muke so ayi mana wani gyara a kasafin an yi mana kuma gun da muke da buƙatar gwamnati ta tallafa akan ilimin yara mata mun shigar da buƙatarmu.

Tun yaushe ne kike bada gudunmawa a kungiyance a Jihar Jigawa?

Tun daga 2012 har zuwa yau babu shekarar da ba mu bada gudunmawa ba a wajan harkar kasafin kuɗi a Jihar Jigawa. Muna bayar da gudunmawar da ake da buƙata tun daga farko har zuwa ƙarshe.

Kuma ƙungiyoyi suna bibiyar kasafin kuɗin har sai yadda aka karanta da yadda ake aiwatar da shi a aikace, suna bibiyarsa har zuwa ƙarshen shekara, domin tabbatar da cewar abinda gwamnati ta ce za ta yi a makarantu ta yi, in ba ta yi ba me ya hana ayi shi kuma muna sa ido.

Ina alfahari da nufin kirki cewar duk nasarar da aka samu a Jihar Jigawa a ɓangaren ilimi ‘yan ƙungiyoyi sun taimaka wajan haɓakar ilimi a Jihar Jigawa.

Shin shirye-shiryen radiyo ko ya taimaka wa ƙungiyarku wajan wayar da kan jama’a?

Gaskiya shirye-shiryen radiyo ya taimaka mana matuƙa wajan wayar da kan jama’a wajan fito wa a faɗa wa gwamnati gaskiya akan matsalolin ilimi da rashin kula da haƙƙin malamai da gyaran makarantu tare da ɗaga darajar malamai. Kuma an samu gyararraki ba laifi gaskiya.

Muna bibiyar ayyukan gwamnati idan gwamnati ta ce za ta bai wa ‘yan makaranta ‘uniform’ 10,000 muna bi muna gani, su waye suka samu ‘uniform’ ɗin kuma nawa aka raba wa yaran su nawa ne suka anfana kuma nawa ne suka ci moriyar kayan.

Mu ne muka yo ‘adɓocacy’ gwamnati ta kafa ƙungiyoyin malamai da iyayen yara( SBMC) SAMADA. ƙungiyoyi 500 a Jihar Jigawa su ne har gobe ake cin moriyarsu a jihar nan.

Wanne abu ne a lokacin da kike gwagwarmaya ba za ki manta da shi ba?

Na sha wahala a aikin da mukayo a garin Malam da ke ƙaramar Hukumar Maigatari da Dadumadumi Toka da ke ƙaramar Hukumar Kafin Hausa saboda kafin gwamnatin APC ta yi titin Balungu zuwa Kafin Hausa dumadumi toka ba ta da hanyar mota, ƙauye ne da yake da nisa daga Kafin Hausa 

Mun sha wahala matuƙa alokacin da muka je Dumadumi saboda hanyar ta kasace mai cike da rairaiyi da ƙayoyi wadda take da matsaloli masu yawa, haka zalika garin Malam da ke Maigatari shi ne ƙauyen da na sha wahalar da ba zan mantaba. Don na faɗo daga mashin har na yi birgima a rairayi da yake Sahara ne.

Alokacin da na je aikin ƙungiya mun gano garuruwa da suke da matsaloli na ƙarancin yara mata da ke yin karatun boko da suka haɗaa da Jabarna, Dumadumi Toka,da garin Malam da auyukayi .

A wancan lokacin daga cin Dumadumi Toka Malam Adamu Abdullahi Toka wanda shine hedimasta na farko a makarantar primary ta garin ya kira ni ya gayamin cewar suna da matsala a garinsa, wato Dumadumi Toka musamman akan karatun yara mata. Ya ce wallahi babu mace ɗaya da ta kammala karatun digiri wadda suke da makarantar sakandire sama da shekaru hamsin. 

Don haka ya gayyace mu muka je Dumadumu domin mu wayar da kan jama’a muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata. 

Haka zalika a ƙauyan Jabarna da ke ƙaramar Hukumar Jahun akwai wata rana da na je ƙauyan Jabarna, muna shiga garin ni da ɗan achaɓa .uka faɗa wani furunfurmi, wato wani rami mai cike da ruwa, ruwa iya wuyana, sai da ɗan achabar nan ya kama hannuna ya fito da ni. 

Alokacin yara ‘yan makaranta sun taso daga makaranta shine yaran suka kewaye ni, suna ihu wayyo Allah malama ta faɗa a kwata, ta faɗa akwata. Haka ya sa mutane manya suka fito daga gidaje suka kewaye ni alokacin da dagaci yazo yaga nice sai kunya ta kamashi, bai iya haɗa ido da ni ba. Haka na fita na je gidansa matarsa ta zuba min ruwa na yi wanka, taban rigarta nasa, na fito aka yi taro a aka gama na dawo Dutse washe gari na koma na mayar mata da rigarta.

Kuma Malam ka sani fa ba albashi ne da ni ba, duk wannan ƙoƙari da muke yi muna yi ne domin mu samu cigaban karatun yara mata a Jahar Jigawa.

Yayinda a garin Malam a ƙaramar Hukumar Maigatari mun je ni da ciyaman ɗin ƙungiyarmu marigayi Malam Zakari Muhd Babur, zuwa ƙauyan garin Malam, hanya ce da take cikin sahara wadda take da tarin rairayi da take da wahalar bi akan babur, anan ne babur ya ‘yar da ciyaman a rairayi ina tausayamar ban yi auni ba ni ma nawa babur ɗin da na hau ya yi wurgi da ni na yi ta birgima sai wata bishiya ce ta yi min birki alokacin da nake birgima ciyaman yana kallon yadda nake birgima shine ya taso cikin tsoro da damuwa ya kama hannuna yana tambayata ince dai ban ji ciwo ba, na ce mar ban ji ba.

Kuma a lokacin na ji rauni aƙafata na ƙone aƙafata wadda haryanzu akwai rami a ƙafata.

Yayinda na je Auyo da damina sukuma a ƙauyan Auyo kayi da zarar ance damina ta faɗi karatun ya’yansu tsayawa ke yi basa zuwa makaranta muka haɗa ƙarfi da ƙarfe ni da ‘yan garin muka siyi katako aka yi gada aka yi cikin buhun ƙasa a ka samu hanyar da yara suka bi zuwa makaranta.

Wannan ya sa har gobe inna je Auyokayi za ka ji ana maraba da zuwa Nafisa. Ni ýar gida ce a Auyokayi kowa yasan haka .

A wancan lokacin kamar ƙauyuka nawa ne kukabyi aiki?

Garuruwan da muka yi gangami da faɗakarwa a wancan lokachin sun haɗa da Unguwar Garko a Hadejia, Auyokayi a Auyo, Garin malan a Maigatari, Dumadumin Toka a Kafin Hausa, Jabarna a Jahun, Kanjua B a Gumel, kafin baka normadic primary school kiyawa, Matara Uku community a Birniwa, Roni, da Gagarawa.

Sauran su ne akwai Islamic Junior Secondary Gwaram mu muka sa wani bawan Allah ya gina ta da ‘toilets’. Gwamnati ta gina ‘toilet’ a JSS ɗan Bulama bayan mun yi ‘town hall meeting’ a Gagarawa LGA.

Za mu ɗora daga inda muka kwana. A mako mai zuwa za mu ji dalilin da ya sa Hajiya Nafisa ba ta tsaya ta yi aikin akawun ba ko banki, maimakon haka ta zaɓi zama ma’aikaciyar sa kai a ƙungiyoyi.

By ukarofi