Majalisar Dokokin Katsina za ta samar da dokar hana ƙwacen waya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokoki ta Jihar Katsina za ta samar da doka da za ta tanadi hukunci mai tsanani ga masu kai hare haren ƙwace waya a jihar.

Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Funtua Hon Abubakar Muhammad Total ya gabatar da ƙudirin haka a gaban majalisar.

Ya nuna takaicin sa kan yawaitar masu kai hare haren ƙwacen waya ga al’umma a yankin sa na ƙaramar hukumar Funtua,wanda sanadiyyar haka ake rasa rayuka.

Akan haka ne ya buƙaci majalisar ta samar da dokar da za ta tanadi hukunci mai tsanani ga masu aikata wannan mummunan ɗabi’a.

Ɗan majalisar ya bada misali da wani harin ƙwace waya da aka kai wa wani da asuba ya fito za shi masallaci a garin Funtua inda nan take suka daɓa masa wuƙa ya mutu.

Gabatar da ƙudirin ke da wuya gaba ɗaya ƴan majalisan su ka nuna goyon bayansu akan ƙudirin,domin a cewar su ƴan majalisar wannan lamari ya shafi duk jihar baki ɗaya.

Daga ƙarshe majalisar ta amince da a samar da doka da za ta tanadi hukunci mai tsanani ga masu wannan muguwar ɗabi’a.

By ukarofi