Dalilin da ya sa muka hamɓarar da gwamnatin Buhari a 1985 – IBB

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ce an hamɓarar da gwamnatin Muhammadu Buhari ne saboda rashin gamsuwa da manufofi da salon shugabancinta.

Babangida shi ne shugaban ma’aikata na Buhari wanda ya hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari a juyin mulkin ranar 31 ga Disamba, 1983.

A cikin littafin tarihinsa mai suna ‘A Journey In Serɓice’ wanda aka ƙaddamar a Abuja ranar Alhamis, IBB ya ce gwamnatin Buhari ta fitar da wasu ‘yan ta’adda waɗanda suka kai ga cin zarafin ‘yan ƙasa.

Ya ce, ya yi imanin manufofin Buhari da mataimakinsa, Tunde Idiagbon, “suna kawo cikas ga ci gaban al’umma” kuma rashin gamsuwa “daga ƙarshe ya kai ga hamɓarar da ita a 1985”.

“Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya maye gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari da mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari, Ibrahim Babangida ya ɗauki muƙamin babban hafsan soji.

“Sai dai kuma ya ƙara nuna rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Buhari da salon shugabancin da ya yi imanin na da illa ga ci gaban ƙasa. Wannan rashin gamsuwa daga ƙarshe ya kai ga hamɓarar da shi a shekarar 1985, kuma ya karɓi mulki a matsayin shugaban ƙasa na soja,” inji littafin.

Yayin da ya ke tunawa da yadda ya yi tattaki daga Minna zuwa Legas a ranar 27 ga watan Agusta, 1985, domin karɓar ragamar mulki, Babangida ya ce tuni aka fara samun zaman ɗar-ɗar tun farkon wannan shekarar kuma ya zama dole a samu canjin shugabanci.

Tsohon shugaban na Nijeriyar ya ci gaba da cewa juyin mulkin da ya kawo Buhari kan karagar mulki, wanda ya bayyana a matsayin “aiki ne na ceto” ya sa sojoji suka yi ƙasa a gwiwa.

“A wannan ranar, ya zama ra’ayi na na shiga cikin sirdin shugabancin ƙasa a madadin sojojin Nijeriya. Canjin shugabanci ya zama dole a matsayin mayar da martani ga taɓarɓarewar yanayin al’umma da damuwa game da makomarmu ta al’umma. A duk tsawon ranar da muka taso daga Minna muka bi ta Legas zuwa Bonny Camp, na yi tunani sosai kan yadda mu al’umma muka kai ga wannan matsayi da kuma yadda na tsinci kaina a wannan yanayi na ƙaddara,” IBB ya faɗa a cikin littafinsa.

Ya yi ikirarin cewa Buhari da Idiagbon “sun nuna halin ‘mafi tsauri”, inda suka ware kansu daga abin da ake nufi da shugabancin gama-gari.

Ya ƙara da cewa mutum biyun sun sa al’ummar ƙasar suka fara gaba da soji.

By ukarofi