Hon. Abdulmumin Ari ya bada tallafin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin WAEC ga ɗalibai

Spread the love

Daga JOHN WADA KEFFI

A ranar Juma’a ne ɗan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa da Toto a majalisar kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin masarautun gargajiya, Hon. Abdulmumin Ari ya bada cekin zuzuruntun kuɗi har sama da Naira miliyan 45 don a biya kuɗaɗen jarabawar WAEC na ɗaliban sakandare dake ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.

Babban taron tallafin ya gudana ne a filin wasa na tsohuwar kasuwar Keffi.

Da ya ke jawabi a wajen taron Hon. Ari ya bayyana cewa tsawon shekaru biyar kenan da ya ke irin wannan aikin na agaza wa ɗaliban mazaɓarsa a duka matakai don cika alkawuran da ya yi a baya.

Ya ce, ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen yara marasa galihu domin ba su damar cimma mahimman burikansu na samar wa ‘ya’yansu ilimin zamani da na addini.

Honorabul Abdulmumin Ari ya kuma yi alƙawarin cigaba da wannan aikin na agaza wa al’ummar nasa musamman a fannin ilimi, inda ya buƙaci duka ɗaliban da suka amfana da karamcin a karon nan da su tabbatar da sun yi amfani da shi yadda ya dace kana su maida hankulansu a yayin karatun da al’amuransu na yau da kullum.

By Babaji