Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sauran makarantun da za su shiga cikin shirin sun haɗa da makarantun kimiyya da fasaha da kuma kwalejin ilimi na gwamnatim tarayya da ke faɗin kasar.
Shugaban kwamitin TETFUND na majalisar dattijai,sanata Muntari Ɗandutse ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce wannan shiri da haɗin gwiwa da bankin cigaban Afrika da gwamnatin tarayya ne za su gudanar da aikin.
Sanata Ɗandutse ya bayyana cewa da zarar an kammala aikin gina tashoshin, jami’o’i da sauran manyan makarantu na gwamnatin tarayya za su sami saukin yawaitar ɗauke wutan lantarki.
“Haka kuma zai taimaka wa makarantun amfani da kuɗin wutar lantarki da suke biya a duk wata zuwa wasu aikace-aikace”inji sanata Ɗandutse.
Jam’iyyar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya na biyan Naira miliyan 200 duk wata a matsayin kuɗin wutar lantarki da suke sha a cewar Ɗandutse.
Sanata Muntari Ɗandutse wanda shi ke wakiltar shiyyar Funtua a majalisar dattijai ya ce har ila yau hukumar TETFUND za ta gina cibiyar koyon sana’o’in hannun a wasu kananan hukumomi da ke shiyyar ɗan majalisar.
