MOPPAN ta nemi haɗin gwiwa da jakadan Philippines

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagororin Ƙungiyar Ƴan fim ta Ƙasa (MOPPAN), suna ƙoƙarin faɗaɗa harkokin ƙungiyar don janyo ra’ayoyin masu kallo a faɗin sassan duniya daban-daban.

A ƙoƙarinta na haka ne, MOPPAN, a ƙarƙashin jagorancin Malam Umar Mai-Kuɗi ta yanke shawarar miƙa takardar buƙatar haɗa hannu ga Jakadan ƙasar Philippines a Nijeriya, Mista Merleso J. Mallejor don bunƙasa harkokinta a Nijeriya da wajenta.

A sanarwar da sakataren yaɗa labaranta, Ibrahim Amarawa ya fitar, ya ce ƙungiyar a shirye ta ke ta haɗa gwiwa da ƙungiyoyin gwamnati da masu zaman kansu wajen ganin inganta ayyuka.

Ya ce za su yi hakan ne musamman wajen ganin masana’antar Kannywood ta yi fice ta yadda za ta fi shahara a cikin gida Nijeriya da ma ƙasashen waje.

By Babaji