Ramadan: A yi wa ƙasa addu’ar neman zaman lafiya da samun sauƙin rayuwa, inji Maituraka

Spread the love

Daga ABDULLAHI Muhammad a Katsina

Mataimaki na musamman a ofishin mataimakin shugaban majalisar Dattijai Abdulaziz Maituraka ne ya yi wannan kira a lokacin da yake miƙa wa mutane 500 abincin buɗe baki a gidan sa da ke Katsina.

Haka kuma yayi kira ga al’ummar jihar Katsina da su tashi tsaye wajen gudanar da addu’ar samun zaman lafiya da kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

Maituraka ya bayyana cewa matsalar ta’adanci a Jihar Katsina da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa addu’a ne kawai za muyi a wannan wata mai albarka na watan Ramadan.

Kan abincin da ya fara rabawa kuwa ya bayyana cewa a kullum zai ciyar da mutane 500 da abincin buɗe baki ga masu gudanar da azumi har zuwa ƙarshen watan Ramadan.

Sai yayi kira ga masu wadata a faɗin ƙasar nan da su tallafawa marasa shi a cikin wannan watan Ramadan,wata mai albarka.

Maituraka ya bayyana cewa ta wannan hanyar ciyarwa a cikin wannan wata mai albarka, mabuƙata za su sami sauƙin gudanar da azumi cikin natsuwa.

By ukarofi