
Daga BELLO A. BABAJI
Iyalan ɗan TikTok, Ahmed Ataye Na-Madina, wanda ake kira da Titanic, sun barranta kawunansu daga kalaman ɓatancin da ya fitar ta kafar soshiyal mediya.
A halin yanzu, Na-Madina yana tsare a hannun hukuma, a Jos, Babban Birnin Jihar Filato.
A wani faifan bidiyo, an ga inda mahaifinsa wanda ba a bayyana sunansa ba, yana cewa, suna neman masana’antar Kannywood da ta yafe wa ɗan nasu kuma suna alla-wadai da abinda ya aikata.
Ya roƙi jagorori da mambobin masana’antar da su yi haƙuri su yafe masa albarkacin watan Ramadan da al’umma suke gudanar da azumi a cikinsa.
