Gwamnatin Katsina za ta yi haɗin gwiwa da ƙungiyar haɗin kan Funtua don nema wa matasa aiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai bawa gwamna shawara kan samar da aikin yi ga matasa, Alhaji Yau Noa,ya sha alwashin haɗin gwiwa da ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua domin samar wa matasa aikin yi.

Yayi wannan magana ne lokacin da shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua malam Mannir Suleiman da wasu ya’yan ƙungiyar suka kai masa ziyarar ban girma a Katsina.

Ya ce,ya kamata a sami kyakkyawan fahimta tsakanin hukumar sa da ƙungiyar domin gano tare da taimakawa matasan jihar da suke da hazaƙa.

Alhaji Ya’u ya bayyana cewa akwai guraben aiki irin su aikin ɗan sanda,soja,da sauran jami’an tsaro na farin kaya da jihar ke asarar saboda rashin wayar da kai na yadda matasa za su nemi aikin.

Ya tabbatar masu da cewa ofishin sa zai yi aiki kafaɗa kafaɗa da ƙungiyar domin tabbatar da yankin Funtua ta amfana da damar da gwamnatin tarayya da na jiha ke badawa na ɗaukar ma’aikata a jihar.

Tunda farko a jawabin sa shugaban ƙungiyar Mannir Suleiman ya bayyana cewa an kafa wannan ƙungiya ne domin haɗa kan al’ummar yankin Funtua da kawo cigaba a fannin ilimi,kiwon lafiya da aikin jin ƙai a yankin.

Ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina kan ciyar da yankin Funtua da Jihar Katsina gaba musamman gina manyan hanyoyi da gyaran asibiti da sauran su.

Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga al’ummar yankin Funtua da jiha baki ɗaya da su ba gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya kan tsare tsaren ta na ciyar da jihar gaba.

By ukarofi