Majalisar zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da kashe Naira biliyan 2.1 domin samar da kayan aiki a babban asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ATBUTH, dake Bauchi. Abubuwan da za a samar sun haɗa da na’urar X-ray mai ɗaukar hoto ta tafi-da-gidanka, da kuma gyara da samar da kayan aiki na na’urar bincike ta computerized tomography (CAT scan), wato 64-slice CT scan.

Ministan Lafiya , Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana haka yayin da yake wa ‘yan jarida bayani a ƙarshen taron majalisar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

