Watan Ramadan: Rage tambayar kuɗi wurin miji ma sadaka ce

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

‘Yan uwa mata barkanmu da kasancewa a shafin iyali na wannnan mako, domin dai na sani wannan rubutun mata ne za su fi karanta shi, kuma kaso mai ɗan dama da jin haushin taken darasin namu, “ga ‘yar kwangilar mazajenmu” ko.

Idan kun bi ni a sannu za ku fahimci inda muka sa gaba, wanda hakan zai saɓa wa tunanin ku.

Yana daga cikin haƙƙin mace na daga haƙoƙƙin da suka rataya kan mijinta, samar mata da ababen buƙata na yau da kullum, don haka bai zama laifi ba idan mace ta nemi wani abu daga wurin mijinta ba. Kuma wajibi ne ya yi mata matuƙar yana daga cikin ababen dole kamar ci, sha da sutura.

Da wannan zan soma da kira ga mazan da su ji tsoron Allah yayin sauke nauyin da yake kansu na matansu, musamman ma a cikin wata mai tsarki, watan Ramadana, wanda aka so idan kana da kyau ka ƙara da wanka, wato a samu ƙarin kyautata wa iyali a cikin watan.

Kamar yadda aka sani, mai azumi na tare da ‘yan buƙatu na samun sauyi a baki, na daga ɗan abinda baki zai yi marmari da kuma ƙauracewa wasu daga cikin abincin da aka saba ci.

Wannan ya sa yake da matuƙar muhimmanci idan Allah Ya sawwaƙe maka ya kai maigida to a ba wa bakin iyali daɗi a tsayin watan na Ramadan. Idan kuwa hakan ba zai samu ba, to a duba a ga abinda zai iya yiwa, koda sau ɗaya ne a sati.

Ka tuna da cewa, babu inda ciyar da iyali ya taɓa zama sanadiyyar karyewar arziki, sai dai ya zama silar ƙaruwar sa. Don haka idan ka ba su, Allah zai ƙara ma, idan ka nemi matsar da su da sunan tattali, sai Allah Ya bar ka da iyawar ka.

Ku tuna cewa, ciyar da iyalai duk da kasancewar sa wajibi akan miji, Allah Ya yi alƙawarin lada ga yin hakan. Haka ma idan aka kyautata masu bisa ga sauke haƙƙin, maigida zai samu ƙarin buɗi, ƙarin lada, da kuma ƙarin ƙima a idon iyalan nasa.

Idan muka koma ga darasin namu, uwargida da za ta yi duba ga yadda matsin tattalin arziki ya yi wa ƙasar nan ɗaurin minti, ga mai hankali, abin dubawa ne kafin ta tambaye mijinta wani abu. Hujja ce karɓaɓɓa a wurinta yayin da ya ce babu.

Sau da yawa fitinar mata ga mazajen ne ya fi tayar masu da hankali fiye da hauhawar farashin kayayyaki. Wani bawan Allah da an ce masara ta tashi, ba wadda zai tuna gabanshi ya faɗi sai matarshi, don ya san ba za ta yi masa uzuri ba idan ya kasa kawo abinda ya saba.

A ‘yan watannin baya, na je wata gaisuwar mutuwa, lokacin sallah ya yi na fito waje alwala, a wurin na tarar da wata baiwar Allah waya a kunnenta, fuskanta a murtuƙe alamar ranta a ɓace yake.

Da ta fara magana sai na fahimci ababe kamar haka; da ‘yarta take waya, kuma mahaifinta ne ya kawo loka ɗaya na shinkafa saɓanin loka ɗaya da rabi da ya saba kawowa. Cikin fushi uwar ke ba wa ‘yar umurnin kada ta yarda ta dafa abincin, ta ɗauki shinkafar ta mayar wa da mahaifinta da ita. Na fahimci ‘yar na ƙoƙarin yi mata bayanin uzurin mahaifin nata da ya sanar da ita da kuma rokon da ya yi na a yi haƙuri a dafa a hakan. Na fahimci hakan ta yadda uwar ke faɗar, “ba zan saurari uzurin nasa ba, ke zai gaya wa hakan don ke ‘yarshi ce, amma ni ya isa ya nufo ni da wannan shinkafar. Ban amince ba kuma ban yarda ki dafa shinkafar ba, in yana son a dafa ya je ya ƙaro yadda ya saba.”

Ba ina ƙoƙarin yi wa wannan mata hisabi ba, domin ban san irin nata miji ba kuma ban san dalilin ta ba, amma koma meye halinshi, ko me ye dalilin tunda har ya kai ga roƙon ‘yarshi, ya ci ta kawar da kai ta bari a dafa.

Kuma ga duk namijin da zai kawo abinci har ya roƙi iyalinsa su karɓa, to wallahi yana da sauƙi-sauƙi, duba da irin mazan da suka yi yawa a wannan zamani waɗanda ba su ma damu da buƙatun gidansu ba. Wani ma yana da shi ɗin, amma sai dai ya bayar a waje, iyalinshi ko oho. Wani ma fatan yake ku yi ƙorafi ya ɗauke abinda ya kawo don dama dole ce ta sa shi kawowa.

Don haka duk wacce ta kalli yanayin matsi da ake ciki, ta tausaya wa mijinta ta hanyar rage tambayar buƙatunta, ko ta yi amfani da abin da take da shi wurin cike giɓin da aka samu sanadiyar halin da ake ciki, to tabbas tana da lada ta musamman, sakamakon abinda ta yi zai iya shiga layin sadaka mai gudana, wato matuƙar ana amfani da abinda ta yi, za ta ci gaba da samun ladar shi. Amma fa sai ta kauce wa yi wa miji gori, wanda shi ke cinye wa mata lada sau da yawa.

Ki yi don Allah, ki tausaya don Allah, kuma ki karɓi uzurin mijinki idan ya ce babu, saboda Allah, shi kuma Allah zai saka maki ta inda ba kya tsammani.

By ukarofi