
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu raba adadin wutar lantarki mafi girma a tarihin Nijeriya, wanda ya kai megawat 6,003.
Ministan Wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a wata takarda da Mai taimaka masa akan Sadarwa, Bolaji Tunji ya fitar, inda ya ce hakan wata gagarumar nasara ce a lokacin da Nijeriya ta samu adadin megawat 5,801.84 wanda ke ba ta damar raba lantarki na megawat 128,370.75 a kullum.
Ya ce, waɗanda nasarori suna wakiltar bunƙasa da ɓangaren ya samu don biyan buƙatu na wuta ga al’ummar ƙasa da kuma ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da samu wadataccen raba wuta a Nijeriya.
Ya kuma ce, suna fatan hakan ya ɗore da kuma samun ƙari akan haka a ƴan kwanakin nan.
Ya ƙara da cewa, hakan wata shaida ce da ke nuna yadda jagorancin ministan ke ƙoƙari da jajircewa gami da samar da sauye-sauye a harkar lantarkin Nijeriya, wanda hakan ya zama albishir ga goben ƙasar da al’ummarta a yayin harkokinsu.
Har’ilayau, ya ce sun samu nasarar ne bayan haɗa hannu da masu-ruwa-da-tsaki a ɓangaren wajen magance matsalolin da suka jima suna haifar da tsaiko, ta hanyar yin wasu gyare-gyare, faɗaɗa mitoci, ƙaddamar da wasu ababen fasahar zamani don tabbatar da samun wadatuwar lantarki da kuma adalci.
