Dujiman Katsina ya samar wa matasa aiki a hukumomin tsaro na ƙasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai kuma Dujiman Katsina, Hon. Abdullahi Aliyu ya samar wa matasa 175 aiki a hukumomin tsaro.

Hukumomin sun haɗa da hukumar kashe Gobara ta ƙasa, ƴan Sanda, Sojoji, Asibitin gwamnatin tarayya da Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya.

Ɗan majalisar, wanda shi ke wakiltar Musawa da Matazu ya ce, mutane 42 sun samu aiki a hukumar kashe gobara ta ƙasa, sai wasu 18 a hukumar shige da fice, sai kuma mutane 100 a Soja da sauran ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.

A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan yaɗa labarai, Mr Francis Sardauna, ya ce canza rayukan matasa da Dujiman ya yi ya nuna cika burinsa ta hanyar samar masu da aikin yi.

Da yake miƙa takardun kama aiki ga matasan, Ɗan majalisar ya sha alwashin kawo ƙarshen fatara da rashin aikin yi a mazaɓarsa.

Ya ce, ayyukan da ya samar wa matasan ba shi da wata alaƙa da siyasa, sai dai ƙoƙarinsa na inganta rayukan al’ummar mazaɓarsa.

Ya yi alƙawarin samar wa duk wani yaro da ya kammala karatun digiri, aiki ko taimaka masa da tallafi na kama sana’a da zai dogara da kansa.

Dujima ya kuma taya matasan murnar samun aikin tare da jan hankulansu da su sadaukar da kai tare da nuna ƙwarewa a duk inda akai kai su aiki.

By Babaji