Gwamnan Katsina ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙin yin sulhu da ƴan ta’adda

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya sake nanata matsayin gwamnatinsa na ƙin sasantawa da ƴan ta’adda da suka lalata wasu sassan jihar.

Ya faɗi haka ne a garin Jibiya a lokacin ƙaddamar da bada tallafin kayan abinci da Ɗan Majalisar Dokoki na jihar, Hon. Mustapha Yusuf ya samar wa al’ummar mazaɓarsa.

Ya ce, gwamnati ba za ta sasanta da yan ta’adda ba, amma ƙofa a buɗe take kan duk wanda yake son ya ajiye makamansa.

“Gwamnati na maraba ga duk ɗan ta’addan da ke son aje makaminsa domin shiga cikin al’umma ya cigaba da rayuwarsa kamar yadda ya ke da.”

Ya yaba wa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Dikko Raɗɗa ya kuma yaba wa Ɗan majalisar bisa ƙoƙarin da ya yi na raba kayan abinci da kuɗi ga tsofaffi da marasa ƙarfi a yankin.

Ya yi kira ga sauran ƴan majalisu da masu wadata da su fita su bai wa irin waɗannan mutanen taimako a cikin wannan wata mai albarka na watan Ramadan.

By Babaji