Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa na yunƙurin dakatar da Sanata Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattawa na duba yiwuwar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.

Hakan ya biyo bayan bincike ne da kwamitin ladabtarwa na majalisar ya gudanar a kanta, wanda ya ce an same ta da karya wasu daga cikin dokokin majalisar.

Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya ce za a rufe ofishinta da kuma haramta mata zuwa farfajiyar majalisar a yayin dakatarwar.

Sannan, za a daina biyan ta kuɗaɗen albashi da na mataimakanta zuwa lokacin da wa’adin zai ƙare.

Kazalika, za a hana ta wakiltar Nijeriya a kowane aiki a matsayinta na sanata, duk a cikin lokacin.

Har’ilayau, Sanatar, mai wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya sai ta rubuta takardar bada haƙuri da neman yafiya don a yi nazari game da dakatarwar tare da jin ra’ayoyi gabannin haka, kamar yadda kwamitin ya bayyana.

By Babaji