
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida kan rikicinta da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
Akpabio ya bayyana hakan a lokacin hukunci kan sakamakon binciken kwamitin ladabtarwa, wanda ya nuna cewa Natasha ta saɓa wa dokokin tsayawa na 2023 na majalisar.
Duk da cewa, wasu daga cikin sanatoci sun yi ƙoƙarin ganin an rage adadin lokacin dakatarwar zuwa watanni uku, amma hakan bai samu ba saboda mafiya rinjaye sun tafi akan hukuncin farko.
Ana ganin cewa akwai yiwuwar a rage adadin lokacin ko kuma a soke dakatarwar baki ɗaya matuƙar Natasha ta rubuta wasiƙar bada haƙuri da neman yafiya.
Bayan haka ne, Natasha ta samu rakiyar jami’in kula da oda, inda aka ji tana cewa wannan rashin adalcin ba zai ɗore ba.
A ƴan kwanakin nan ne Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta miƙa takardar ƙorafi na cin zarafin ta akan Akpabio, wanda haka ya haifar da cecekuce.
A nan ne Mai Tsawatarwa, Mohammed Monguno ya tsawatar game da dokar tsayawa ta 40 a majalisar, ya na mai cewa ba za a saurari batun ba tunda an shigar da ƙara a kai a kotu tsakanin Sanata Akpoti-Uduaghan da matar Sanata Akpabio.
Haka kuma, saboda ita da kanta ta sanya wa ƙorafin hannu a madadin wani ya yi a madadin ta, kamar yadda dokar majalisar ta tsara.
