
Daga BELLO A. BABAJI
Matar Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce Majalisar Dattawa ta na ɗaukar matakan da suka dace game da zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
A lokacin da ta ke tsokaci kan batun a Abuja, ranar Alhamis, Sanata Remi ta ce, Majalisar Dattawa a matsayinta na babbar zauren dokoki a Nijeriya, waje ne da bai kamata a ce irin haka ya faru ba.
Ta ce, lallai ta na sane da abinda ke faruwa a majalisar kuma jagororinta suna ɗaukar matakan da suka dace akan al’amarin.
Ta kuma ce, majalisar waje ne mai girman daraja don haka akwai buƙatar a girmama ta, ta na mai cewa abin alfahari ne a ce mutum ya tsinci kansa a matsayin ɗaya daga cikin mambobinta, kasancewar ta yi shekara 12 a zauren.
Akan batun ne majalisar ta ɗauki matakin dakatar da Sanata Natasha bisa saɓa wa dokokin tsayawa na majalisar na 2023, biyo bayan rahoton kwamitin ɗa’a da ladabtarwa.
