APC ta bai wa gwamnan Ribas sa’o’i 24 ya sauka daga kujerarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ana cigaba da samun rashin jituwa a harkokin siyasar Jihar Ribas bayan da jagorancin Majalisar Dokoki ɓangaren Kakaki Martins Amaewhule ya ƙi amsa gayyatar Gwamna Siminalayi Fubara.

An shirya zaman ne da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin a Gidan Gwamnatin jihar, inda ƴan majalisar suka yi buris tare da cigaba da gudanar da harkokinsu a majalisar.

Tun a ranar Lahadi ne alamu suka bayyana cewa ba za su amsar gayyatar ba, bayan ganin ɗaya daga cikin su a wani faifan bidiyo ya na mai sukan batun gayyatar da gwamnan ya yi masu.

Sa’o’i 48 da ƴan majalisar suka bai wa gwamnan na ya miƙa Kasafin 2025 ya cika, inda daga nan ake ganin za su fara yunƙurin neman tsige shi.

Hakan ya biyo bayan saƙon da shugaban APC na ɓangaren a jihar, Cif Tony Okocha ya aika, wanda ke neman Gwamna Fubara ya yi murabus, ya na mai bada misali da hukuncin Kotun Ƙoli, inda ya ce babu wani zaɓi da ya rage masa illa ya sauka ko a tsige shi.

Haka kuma, majalisar ta bada izinin a kamo Shugaba Hukumar Zaɓe ta jihar (RVSIEC), Mai Shari’a Adolphus Enebeli (mai ritaya) da wasu kwamishinoni huɗu kan ƙin amsa gayyatar majalisar bayan wa’adin kwana uku da ta ba su ya ƙare.

By Babaji