Gwamnatin Katsina ta kashe fiye da Naira biliyan 70 a harkar noma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka lokacin da yake bayani kan nasarorin da gwamnatin su ta samu daga hawan su karagar mulki.

Ya ce gwamnati ta kashe Naira biliyan 36 wajen samar da rarraba tan 20,000 na takin zamani a shekarar da ta wuce.

Ya bayyana cewa bugu da ƙari,an bayar da babura 722 da fanfunan feshi ga malaman gona biyu biyu da aka horar a dukkan mazauna(361) da ke jihar.

“Anyi hakan ne domin a wadata manoman mu da isasshen taki domin tafiyar da aikin noman su”inji Joɓe.

Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 21 wajan sayo taraktoci 400 tare da dukan kayayyakin su da injiunan shuka guda 20,000 da na’urar girbi da shuka guda goma.

Haka kuma gwamnatin Katsina ta kashe Naira Miliyan 790 wajen gyaran wuraren ajiye kayan amfanin gona a shiyya bakwai na jihar, inji Joɓe.

An kuma farfaɗo da cibiyar gudanar da sabon salo da dabarun noma na Shonghai da ke maƙera a ƙaramar hukumar Dutsinma da ya ce farfaɗo da wannan cibiya,zai bada damar yin noman rani da na damina.

Malam Farouk Joɓe ya ce an horar da mata 150 kan noman kayan lambu da ake har haɗa kayan abinci mai gina jiki tare da basu irin zogale guda 54,000 .

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da ba aikin gona kulawa na musamman ganin yadda mafi yawan al’ummar jihar manoma ne.

By ukarofi