Wata annobar cuta da ake zargin sanƙarau ce ta hallaka mutane 26 a Jihar Kebbi. Gwamnatin jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce yankunan da abin ya fi shafa sun haɗa da ƙananan hukumomin Aliero, Gwandu da Jega.
Sanƙarau cuta ce mai tsanani wadda ake ɗauka daga mutum zuwa mutum. Alamomin ta sun haɗa da zazzabi mai zafi, ciwon kai mai tsanani, riƙewar wuya, amai da toshewar ido ga haske.
Gwamnatin jihar tana ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar tare da ba da shawara ga jama’a su riƙa kula da tsafta da kuma kai rahoton duk wanda ke da alamun cutar.
