
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Taraba ta ce Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Alƙali ya tafi ƙasar waje ne domin kula da lafiyarsa.
Tun a watan Nuwamban 2024 ne Alƙali ya bar Nijeriya, wanda hakan ya sa masu-ruwa-da-tsaki a ciki da wajen jihar yin ƙorafi.
Amma, a wata sanarwa da Kwamishinar Labarai da Wayar da kan al’umma ta jihar, Zainab Usman ta fitar, ta ce Mataimakin gwamnan na fama ne da rashin lafiyar riƙewar wani ɓangare na jikinsa da ya kai ga ba ya iya magana.
Ta ce, amma a yanzu ya na samun sauƙi kuma zai koma aiki nan ba da jimawa ba.
Da farko dai, an garzaya da shi ne zuwa Abuja inda daga bisani aka wuce da shi zuwa Cairo, Babban Birnin ƙasar Misira.
Ta kuma ce, rashin lafiya abu ne da ka iya samun kowa, don haka kafin a je kotu domin ta tabbatar da batun lafiyar mutum ko wani babban jami’i, akwai buƙatar a kuma yi la’akari da yanayin ɗabi’a.
Haka kuma, dokar da ke nuna cewa a tsige jagora a yayin da ya kai kwanaki 90 ba ya jiharsa, ta taƙaitu ne akan gwamna ba mataimaki ba.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Bordiya Buma, wanda ya ziyarci Mataimakin gwamnan, ya ce ya na samun sauƙi, kuma suna fatan ya samu waraka a cikin ƙanƙanin lokaci tare da koma wa aiki kamar yadda aka saba.
