Ku dakatar da ƙarin kuɗin cajis na ATM – Majalisar Wakilai ga CBN

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Talata ne Majalisar Wakilai ta umarci babban bankin Nijeriya, CBN, da ya gaggauta dakatar da aiwatar da ƙara kuɗin hada-hadar na’urorin ATM a bankuna.

A lokacin da ya ke magana kan batun gaggawa da ya ɗauki nauyi a majalisar, ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP Edo), ya yi kira da a dakatar da aiwatar da ƙarin har zuwa lokacin da za a yi zama da kwamitin majalisar da ke da hurumin tattaunawa da samar da mafita game da lamarin.

A kwanan nan ne CBN ya aika da saƙon umarni na kwaskwarima da aka yi wa kuɗin cajis a ATM da ake amfani da su a bankuna da makamantansu.

Onobun ya ce, karin zai taimaka wajen ƙara gallaza wa al’umma ta fuskar kuɗi da sauran buƙatun yau da kullum.

Ya ce, karo na ƙarshe da aka yi gyara akan tsarin cazar kuɗin shi ne a shekarar 2019, inda daga N65 aka mayar da shi N35 a kowacce harƙalla ɗaya.

Sabon tsarin da CBN ya bayyana, zai bada dama ga kwastomomi su riƙa cire kuɗi a bankunansu a kyauta yayin da kuma za a riƙa cazarsu Naira 100 a kowane N20,000 da suka cire a wani bankin da ba nasu ba.

Haka kuma, kwastomomin da ke cire kuɗi a wasu wuraren da ba bankuna ba kamar a kasuwanni da makamantansa kuma a ATM na wani bankin, za a riƙa cazarsu N100 da kuma karin wata N500.

Ya koka ganin yadda al’umma ke fama da matsalolin hauhawar farashin kayayyaki na dolen rayuwa wanda ya kai ga rage ƙarfi ga kuɗaɗen da suke samu gami da nakasa tattalin arziƙinsu.

By Babaji