Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Wakilai ta umarci NCC ta rufe shafukan batsa a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Wakilai ta umarci a rufe baki ɗaya shafukan batsa a Nijeriya.

Majalisar ta umarci Hukumar Sadarwa ta NCC da ta gaggauta rufe shafukan a ƙasar.

Ta bada umarnin ne a yayin zamanta na ranar Talata, biyo bayan gabatar da wani batu da ɗan majalisa, Ɗalhatu Tafoki daga Jihar Katsina ya ɗauki nauyinsa.

Sauran bayanai za su biyo baya…

By Babaji