Daga USMAN KAROFI
Kotun ƙoli ta Najeriya ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Agboola Ajayi na jam’iyyar PDP ya shigar kan takarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC a Jihar Ondo.
Alƙalin da ya jagoranci yanke hukuncin, Mai Shari’a Lawal Garba, ya bayyana cewa ƙarar da Ajayi ya shigar ta makara kuma yana da’awar da ba ta da tushe kasancewar ya fito daga wata jam’iyya daban.
Kotun ta tabbatar da cewa batun rikicin cikin gida ne na jam’iyyar da ake ƙara, kuma masu ɗaukaka ƙarar ba su da hurumin (locus standi) na gabatar da irin wannan ƙara.
Ajayi ya yi ikirarin cewa an canza sunan Mataimakin Gwamna Olayide Adelami ba tare da cikakken bayanin sauyin sunan ba, amma Kotun ta ce canjin sunan da aka yi daidai da ƙa’ida ba ya zama laifi ko rashin cancanta a zaɓen siyasa.
Haka kuma, Kotun ta umurci Ajayi ya biya naira miliyan biyu ga kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara huɗu a matsayin kuɗin kotu.
