Ɗangote ya sake rage farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur a defot zuwa Naira 815 a kowacce lita.

Hakan ya biyo bayan saukar farashin man ne a inda ake saukewa zuwa N774.82 ga kowacce lita, wanda ya yi ƙasa da na Matatar Ɗangote da ake bayarwa akan N825.

Kakakin ƙungiyar ƴan kasuwar fetur masu zaman kansu, Chinedu Ukadike ya tabbatar da ci-gaban.

Ragin farashin ya samu ne a yayin hamayya da ake samu kan farashin a tsakanin manyan ƴan kasuwar Albarkatun mai a Nijeriya.

A watan baya ne aka sha samun gogayyar farashinsa, inda Matatar Ɗangote da NNPCL suka yi ta sauya farashinsu.

By Babaji