Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Katafaren Kamfanin man NNPC a Nijeriya ya musanta cewar ya soke yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin ɗangote domin sayar masa da gurɓataccen mai a farashin naira.
Mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya bayyana cewar, yarjejeniyar da suka ƙulla da ɗangote domin sayar masa da man na watanni 6 ne, kuma za ta ƙare ne a ƙarshen wannan wata na Maris.
Soneye ya ce yanzu haka suna ci gaba da tattaunawa da kamfanin domin tsawaita yarjejeniyar.
NNPC ya ce tun bayan fara aikin matatar ɗangote a shekarar 2023, an samar masa da ɗanyen mai ganga miliyan 84 a cikin gida, saboda haka ya yi watsi da zargin cewar ya soke yarjejeniyar ba shi man.
