Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da aka shigar game da mayar da Al-Mustapha Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu har zuwa ranar 6 ga Yuni.
Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ne ya sanya ranar a ranar Talata bayan da ɓangarorin da abin ya shafa suka gabatar da takardar hujjoji a kotu.
Kwamitin Alƙalan ya kuma sanar da cewa duka ɗaukaka ƙara guda huɗu za su bi hukuncin da za a yanke kan ɗaya daga cikin ƙarar.
A baya, lauyan gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu Maikyau (SAN), ya nemi izinin kotu domin gabatar da ƙarin hujjoji a ɗaukaka ƙarar sa da aka shigar a ranar 19 ga Maris, 2025, kan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da aka yanke a ranar 14 ga Afrilu, 2016.
Haka kuma, ya jaddada cewa Babbar Kotun Jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron ƙarar da Jokolo ya shigar a ranar 11 ga Disamba, 2014, don haka shari’ar da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi ba ta da inganci kuma ba ta da wani tasiri a doka.
Sai dai lauyan Jokolo, Sylɓester Imhanobe Esƙ, ya buƙaci kotu da ta yi watsi da ƙarar tare da hukunta Gwamnan Jihar Kebbi, Antoni Janar na Jihar Kebbi, Alhaji Abdullahi Umar, da sauransu da biyan kuɗaɗen da suka dace, bisa gazawarsu wajen gabatar da hujjojin da za su rushe hukuncin kotunan ƙasa da suka tabbatar da cewa gwamnan jihar bai gudanar da binciken da ya dace kamar yadda Sashe na 6 na Dokar Sarakuna (Naɗin Sarauta da Tsige Sarauta) ta Jihar Kebbi ta tanada kafin tsige Jokolo ba.
