An yi garkuwa da wata soja da mutane biyu a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da wata sojar ruwa da ke aiki a Hedikwatar Tsaro a Abuja, wadda ba a bayyana sunanta ba.

An yi garkuwa da ita ne tare da wasu mutane biyu a gidajensu dake unguwar Mpape, kamar yadda wata majiya daga sojoji ta bayyana.

Majiyar ta kuma ce, ƴan bindigar sun buƙaci a biya su miliyan N100 a matsayin kuɗin fansa kafin a sako su.

Zuwa lokacin haɗa rahoton, ba a samu jami’an yaɗa labarai na hedikwatar a waya ba domin ji bakunansu, kuma ba su amsa saƙon kar ta kwana ba da aka aika masu.

Lamarin ya jefa al’ummar babban birnin cikin fargaba game da yadda ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci ya ke ƙara yawaita.

By Babaji